UNICEF: Yara da dama na fama da yunwa
February 21, 2017Wadannan kasashe dai sun hada da Najeriya da Somaliya da Sudan ta Kudu da kuma Yemen, inda babban daraktan asusun ya ce muddin ba a dauki wasu matakai na gaggawa ba to tabbas yara za su kara shiga halin ni 'yasu. Rahoton na asusun ya nunar da cewa a kasar Yemen, inda ake fama da yakin basasa kusan shekaru biyu yara dubu 462 ne ke fama dayunwa mai tsanani, yayin da a Najeriya a yankunan da ake fama da rikicin Boko Haram ake da yara dubu 450 da ke cikin wannan mawuyacin hali na rayuwa.
Matsalar fari a Somaliya ta bar yara dubu 185 da ke daf da fadawa matsalar yunwa, kuma adadin na iya kai wa dubu 270 nan da 'yan watanni masu zuwa, yayin da a Sudan ta Kudu yara dubu 270 ne ke fama da matsananciyar yunwar. Babban daraktan asusun na UNICEF Antony Lake ya yi kira da a dauki matakan gaggawa.