Finland daf cikin NATO
April 3, 2023Talla
Da yake Magana da manema labarai Stoltenberg ya ce ranar ta gobe tana cike da tarihi ga Finland da ma kungiyar tsaron ta NATO. Ya kuma ce yana da kyakyawan zaton a kan ganin Sweden ta samu shiga cikin kungiyar wacce har yanzu Turkiyya ba ta ba da amanarta ba a kanta.Tun da Rasha ta mamaye Ukraine kasashen Finland da Sweden suka yanke shawarar ficewa daga matsayinsu na kasashe 'yan baruwanmu domin shiga kawance na NATO don samun kariya ko da wani abu ka taso.