Turkiya ta cire dokar ta baci
July 19, 2018Talla
Duk da cewa ana cike da fatan samun sukunin al'amura a Turkiyya bayan soke dokar ta bacin, amma 'yan adawa na fargabar gwamnati ta sake tsawaita dokar mai tsanani, 'yan adawar na ganin a baya gwamnatin ta sha tsawaita dokar ta bacin har sau bakwai. Akalla mutane 80,000 aka rufe a gidajen kurkuku yayin da aka kori dubban ma'aikatan gwamnati cikin wa'adin dokar bisa zargin alaka da malamin addinin nan Fetullah Gulen da ke samun mafaka a Amirka wanda gwamnatin Turkiyya ke zargi da kitsa juyin mulkin da ya ci tura.