Tattalin arziki
Belarus: Turkiyya ta rage jigilar fasinja
November 12, 2021Talla
A yanzu dai mahukuntan na Ankara sun bayyana cewa ba za a kara barin wadanda ke dauke da fasfo din kasashen Siriya da Iraki da kuma Yemen su hau jirigin saman Turkiyya ba. A hannu guda suma mahukuntan na Belarus sun sanar da cewa tuni suka fara bin umurnin na Ankara, ta hanyar hana fasinjojin da abin ya shafa shiga jirgin sama mallakar kasar ta Belarus.
Tun da farko dai kungiyar Tarayyar Turan EU, ta yi barazanar kakaba takunkumi ga duk wani kamfanin jiragen sama da ya kwaso 'yan gudun hijira zuwa Belarus, da nufin ba su damar yin amfani da Minsk din domin shiga EU ba bisa ka'ida ba.