Shakku da murna bayan Erdogan ya lashe zabe
June 25, 2018Tun da yammacin ranar Lahadi dubban magoya bayan shugaban kasar Turkiyya recep Tayip Erdogan suka yi ta bukukuwan nuna murna ga samun tagwayen nasarori da suka yi na lashe zaben shugaban kasar da kuma samun rinjaye a majalisar dokoki. Erdogan ya samu kashi 52.5 cikin 100 na yawan kuri'un da aka kada da kuma kashi 53 cikin 100 a majalisar dokoki, wanda zai ba shi damar gudanar da mulkinsa, ganin cewa a yanzu zai yi mulki ne a matsayin shugaban kasa mai cikakken iko.
"Daga yanzu za mu soma aiki domin cika alkawuran da muka dauka wa al'ummarmu, kuma mun kammala shirye-shirye kan abin da ya shafi sabon tsari na shugaban kasa mai cikakken iko."
A fannin yaki da ta'addanci da kasar ta Turkiyya ta sawa gaba, da ma halin da ake ciki a kasar Siriya, shugaban na Turkiyya da ya sake samun amanar 'yan kasarsa ya ce babu gudu babu ja da baya.
"Turkiyya ta kuduri aniyyar yaki da duk wata kungiyar 'yan ta'adda, har da kungiyar PKK da ta FETO, tare da ci gaba da kakkabe miyagu a kasar Siriya, don bai wa bakinmu damar komawa gidajensu."
Yawan masu zabe ya wuce misali
Mutane sama da miliyan 56 ta kamata su yi zaben, kuma kashi 87 cikin 100 na wadannan mutane sun yi zabe, wanda ake ganin wannan adadi ya wuce misali a kasar, kuma a karon farko a tarihinta, 'yan kasar sun yi zabe a rana guda domin zaben shugaban kasa da kuma 'yan majalisar dokoki. Merve Ozcan wata matashiya mai shekaru 18 da haihuwa na cikin murnar samun wannan sakamako.
"Ina cike da farin ciki maras misali. Mun yi ta rokon Allah sosai ba dare ba rana domin mu samu kaiwa ga wannan sakamako. Wannan wani babban ci gaba ne."
Sai dai a wani na birnin Santambul, zuciyoyi sun kasance cike da duhu, yayin da fuskoki suka murtuke, inda ake ganin kallo mai cike da gajiya daga idanun jama'a a bangaren 'yan adawa wadanda ba su boye yadda wannan sakamako ya sanyaya musu gwiwa ba, kamar yadda wannan matar ta fada.
"Gaskiya ban ji dadi ba, na kasance mai cike da tsammanin za mu samu nasara a wannan zabe a wannan karo. Ba na tsammani ko Turkiyya za ta tafi da kyau. Idan kuma gwamnati ta yi la'akkari da wani babban kaso na 'yan kasar da ba su zabe shi ba, domin girka tsari na siyasa mai cike da daidaito, to lokacin ne za mu sa ran samun ci gaba. Sai dai ba na tsammanin hakan za ta kasance."
Aminta da sakamakon zabe
Sai dai daga nashi bangare babban dan takara na bangaren adawa Muharrem Ince, wanda ya zo na biyu a zaben da kashi 30.7 cikin 100, a cikin wani jawabi yayin wani taron manema labarai a birnin Ankara a wannan Litinin, ya ce ya amince da kayen da ya sha, amma kuma ya yi kira ga shugaba Erdogan da ya kasance shugaban dukannin 'yan kasar ta Turkiyya miliyan 81 ba tare da nuna bambanci ba.
Tuni dai Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya aikewa da Shugaba Erdogan wasikar taya murna, inda ya ce wannan nasara ta kara tabbatar da irin kimar da yake da ita a idanun 'yan kasarsa.