Sallar Jumma'a ta farko a Hagia Sophia
July 24, 2020An dai gudanar da sallar Jumma'ar a dadadden katafaren ginin majami'ar nan ta Hagia Sophia da ke zama daya daga cikin gine-ginen tarihi mafi muhimmanci a duniya. Ko da yake ma'aikatar kula da al'amuran da suka shafi addini a Turkiyya ta ce mutane 500 aka sa rai za su halarci ibadar ta wannan Jumma'a amma kimanin mutane dubu 17 ne ciki har da shugaban kasar ta Turkiyya Recep Tayyip Erdogan suka yi dandazo a ciki da harabar masallacin don sallar Jumma'a. Makonni biyu da suka gabata ne dai babbar kotun Turkiyya ta bai wa gwamnati izinin sake fasalin Hagia Sophia din zuwa Masallaci, matakin da ya ci karo da suka da ra'ayoyi mabambanta a ciki da wajen kasar ta Turkiyya.
Claudia Roth ita ce mataimakiyar shugaban majalisar dokokin Jamus, kana guda daga cikin shugabannin siyasa da suka yi tir da matakin, inda ta zargi Shugaba Erdogan da kokarin karkata hankalin 'yan kasar daga matsalolin tattalin arziki da na coronavirus: "Mummunan abu ne a mayar da wannan gini mai ban al-ajabi da a shekara ta1935 shugaban Turkiyya na lokacin wato Kemal Atatürk ya mayar da shi gidan tarihi, a matsayin alamar sabuwar kasar Turkiyya da ta yi daidai da zamani. Amma yanzu Erdogan ya samu izinin mayar da wurin Masallaci. A ganina tsokana ce da ta wuce iyaka."
Shi ma Orhan Pamuk marubuci dan kasar Turkiyya da ya taba samun kyautar Nobel, ya nuna takaicinsa yana mai cewa da yawa daga cikin Turkawa ba sa goyon bayan matakin, amma saboda tsoro ba sa iya nuna matsayinsu a fili: "Muna son mu yi suna, muna son mu yi amfani da addinin Musulunci don neman suna don mu nuna wa sauran duniya cewa mun ki kasashen yamma. Ba na son aike wannan sakon, ina sukar wannan ra'ayi. 'Yan kasa ba sa iya kalubalantar wannan mataki saboda rashin 'yancin fadin albarkacin baki."
To sai dai an samu wadanda suka ji dadi suka kuma yi murna da mayar da majami'ar ta Hagia Sophia Masallaci. Bisa tarihi katafaren ginin Majami'ar da Sarki Justinian ya gina a karni na shida, ya kasance wata alama ta siyasa. A 1453 lokacin da Daular Othmaniya ta karbi iko da birnin Santambul, Sarki Mehmed na Biyu ya mayar da Majami'ar Masallaci. Sannan Kamel Atatürk da ya zama shugaban sabuwar kasar Turkiyya ya yi amfani da gidan ibadar wani muhimmin abin misali, inda a 1935 ya mayar da Hagia Sophia din gidan tarihi, don aike sakon cewa sabuwar Turkiyya kasa ce da babu ruwanta da addini.