Turkiyya na juyayin juyin mulki na 2016
July 15, 2017Kasar Turkiyya na juyayin yunkurin juyin mulki da aka gudanar a ranar 15 ga watan Yulin 2016, wanda shugaban Recep Tayyip Erdogan ya zargi shahararren malamin Musuluncin nan Fettullah Gülen da kitsawa. Majalisar dokokin kasar na zama na musamman da nufin tunawa da mutane 249 suka rasa rayukansu a wannan juyin mulki da ya ci tura.
Fadar mulki ta Ankara ta kama magoya bayan Gülen dubu 50, yayin da ta kori ma'aikata fiye da dubu 100 da ke da alaka da shi daga bakin aiki. Ko da a ranar Jumma'a ma sai da gwamnatin ta Turkiyya ta sallami ma'aikatan gwamnati fiye da dubu bakwai bisa zargin marar hannun a juyin na mulki da aka murkushe.
Abokan adawar Shugaba Erdogan sun zarge shi da neman fakewa da yunkurin juyin mulkin, wajen aiwatar da salon mulkin kama karya don dawwama a kan karagar mulki. Sai dai magoya bayansa sun danganta yunkurin da hanyar tabbatar da dimukaradiyya a Turkiyya.