1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Gurfanar da sojojin Turkiyya kan yunkurin juyin mulki

Mohammad Nasiru Awal AH
May 29, 2017

Janar-janar guda shida na daga cikin jami'an soja 23 da aka fara zama sauraran shari'arsu a birnin Santambul.

https://p.dw.com/p/2dkz8
Türkei Präsident Erdogan
Shugaba Tayyip Erdogan ya lashi takobin ganin bayan masu hannu a yunkurin juyin mulkinHoto: Reuters/A. Zemlianichenko/Pool

A wata kotu da ke a wajen birnin Santambul na kasar Turkiya an bude zaman sauraron shari'ar da ake wa jami'an soja 23 da ake zargi da zama cikin rukunin 'yan birnin na Santambul da suka kulla makarkashiryar juyin mulkin da bai yi nasara ba a lokacin bazarar 2016. Janar-janar guda shida na daga cikin wadanda ake zargi da aikata laifi a kan kasa da kuma alhakin mutuwar mutane 89 wadanda suka gamu da ajalinsu a birnin lokacin yunkurin juyin mulkin. Ihsan Ayanoglu ya rasa dansa a lokacin ya kuma halarci zaman kotun a wannan Litinin.

Ya ce: "Ya kamata a rataye su don hankalin iyalan wadanda suka yi shahada ya kwanta su kuma samu barci. Wadannan sojoji sun ci amanar kasa, sun yi amfani da makaman kasa suka farma mutane da tankokin yaki da bindigogi. Dole a hukunta su."

Sojojin dai na fuskantar hukuncin daurin rai da rai a kurkuku idan aka same su da laifi.