1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Siriya: Harin Turkiyya a yankin arewaci

Binta Aliyu Zurmi
October 9, 2019

Ma'aikatar harkokin wajen Siriya ta yi Allah wadai da matakin da Turkiyya ta dauka na kaddamar da hari a kan Kurdawa da ke arewacin kasar ta Siriya, inda ta bayyana matakin da cewa ya saba da dokokin kasa da kasa.

https://p.dw.com/p/3QzEe
Türkei Militär an der Grenze zu Syrien
Hoto: Getty Images/AFP/B. Kilic

A wata sanarwar da ma'aikatar harkokin kasashen ketare ta Siriyan ta fitar, ta dora alhakin abin da ke faruwa a kan wasu kungiyoyin Kurdawa, inda ta ce an yi amfani da su domin cimma burin Amirka. Jawabin ya kara da cewa kasar Siriya a shirye ta ke ta karbi 'ya'yanta, idan har sun saduda sun aje makamansu. Kurdawan da ke zaune kan iyakar kasar Siriyan da Turkiya dai, na zaman wadanda suka taka muhimmiyar rawa ta hanyar tallafawa Amirka wajen yakar 'yan ta'addan IS a Siriyan.