1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaTurai

Erdogan ya zargi kasashen yamma da yi masa shisshigi

February 6, 2021

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya mayar wa Kasashen Yammacin Duniya martani mai zafi a game da zanga-zangar da dalibai ke yi a kasarsa.

https://p.dw.com/p/3oybh
Türkei Präsident Erdogan in seinem Arbeitszimmer
Hoto: picture-alliance/AA/K Özer

Erdogan ya ce kamata ya yi irin wadannan kasashe su mayar da hankali kan tarzomar da ke wakana a kasashensu.


Daliban jam'iar Bogazici  ta Turkiyya dai sun kwashe makonni suna zanga-zanga domin bijire wa nada sabon shugaban jami'ar da ke da alaka da jam'iyya mai mulki ta AKP da Erdogan ya yi musu.


Sai dai a jawabin da Shugaba Erdogan ya yi a ranar Jumma'a bayan ya fito daga masallacin Jumma'a ya ce bai kamata Amirka wace a kasarta aka tauye hakkin mutane saboda wariyar launin fata ba ta sa masa baki a kasarsa, yana mai cewa duniya fa ba ta manta abin da ya faru a Amirka a zaben kasar da ya gabata ba. Da ya koma bangaren Faransa, Erdogan ya ce ita ma ta ji da kanta ta tunkari masu zanga-zangar ''yellow vest'' da ke kasarta. A don haka shugaban ya ce babu ragi ba ragowa ga masu yi masa zanga-zanga a Turkiyya.