1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: Erdogan ya sake lashe zabe

May 28, 2023

Sakamakon zaben shugaban kasa zagaye na biyu a kasar Turkiyya na nuni da cewa shugaban kasar Turkiyya Racep Tayyip Erdogan ya lashe zaben da ya gudana a wannan Lahadin.

https://p.dw.com/p/4RvDC
Shugaban kasar Turkiyya, Racep Tayyip Erdogan
Hoto: Murad Sezer/REUTERS

Shugaba Erdogan zai sake jagorantar kasar ta Turkiyya na tsawon wasu shekaru biyar bayan samun nasara da kashi 55.4 inda ya kayar da abokin hamayarsa Kemal Kiliçdaroglu da ke da kashi 47.9 a zabe mai cike da tarihi kuma mafi sarkakiya a kasar.

A lokacin da yake ayyana nasararsa a gaban magoya bayansa a wannan Lahadin, shugaban da yake rike da madafun ikon Turkiya na tsawon shekaru fiye da 20, ya mika godiyarsa ga daukacin al'ummar kasar.

Sai dai har yanzu Kiliçdaroglu bai fito ya kalubalanci sakamakon zaben ba, ko da yake ana sa rai jagoran adawar kasar ya yi jawabi nan gaba kadan. Tuni dai wasu shugabannin kasashen duniya suka fara tura sakon taya murnarsu ga shugaban. Sarkin Katar Tamim bin Hamad Al Thani ya wallafa sakon taya murnarsa ga shugaba Erdogan a shafinsa na Twitter. Kawo yanzu dai ba a sanar da nasarar ta shugaba Erdogan a hukumance ba.