1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Darajar kudin Lira ta fadi a Turkiyya

Zainab Mohammed Abubakar
August 19, 2018

Faduwar darajar kudin Turkiyya wato Lira, biyo bayan takunkumin da Amirka ta kakaba wa kasar ya jefa shugaba Recep Tayyip Erdogan cikin wani tsaka mai wuya a fannin tattalin arziki.

https://p.dw.com/p/33Nbk
Türkei Lira Banknoten
Hoto: Reuters/M. Sezer

Wannan dai shi ne karo na farko da gwamnatin Erdogan ke fuskantar babban kalubale na tattalin arziki. Sai dai kwararru a fannin tattalin sun nunar da cewa, tun kafin Amirka ta kakabawa Turkiyan takunkumi, an nemi bankunan kasar da su daga kudaden ruwa, don kaucewa wannan yanayi da aka shiga na faduwar darajar Lira.

Sai dai rahotanni na nuni da cewar, babban bankin kasar ya dauki matakin sakarwa sauran bankuna kudade, a wani yunkuri na ceto kasar daga shiga halin tasku.