1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiyya: Zaben shugaban kasa da na 'yan majalisa

Ahmed Salisu
June 24, 2018

Al'ummar Turkiyya sun kada kuri'unsu a zaben shugaban kasa da na 'yan majalisar dokoki, zaben da shugaban kasar Racep Tayyip Erdogan ke neman wani sabon wa'adi.

https://p.dw.com/p/30B7A
Türkei Präsidentschafts- und Parlamentswahl 2018 | Wahllokal in Istanbul
Hoto: picture-alliance/Anadolu Agency/E. Yorulmaz

Mutane da dama ne suka fito kada kuri'unsu a zaben wanda takara ta fi kamari tsakanin jam'iyyar AKP ta shugaba Erdogan da kuma jam'iyyar nan ta CHP da ke da matsakaicin ra'ayin 'yan mazan jiya. Hukumar zaben kasar ta ce zaben na yau ya gudana lami lafia sai dai ta ce ta samu bayanai da ke nuna cewar wasu mutane na tafka magudi a kudancin kasar inda ta ce za ta gudanar da bincike don daukar matakin da ya dace.