1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya za ta samu wakilci a shari'ar 'yan NAZI

April 12, 2013

Kotun tsarin mulkin Jamus da ke da mazauninta a birnin Kalsruhe ta tsai da hukuncin ba wa wakilan kafafen yada labaru na ketare damar halartar shari'ar 'yan NAZI

https://p.dw.com/p/18FA5
Hoto: picture-alliance/dpa

Babbar kotun ta Jamus ta bai wa jaridar Sabah ta kasar Turkiyya damar halartar zaman sauraron shari'ar 'yan Nazi da suka kashe baki yan Turkiyya.. Su dai kafafen yada labarunTurkiyya da farko sun soki kotun birnin Münich da za ta saurari shari'ar da za a yi wa Beate Zschaepe 'yar raya manufar NAZI ne da kin ba su damar halartar kotun, bayan da ta ce za ta ba da damar yin hakan ga 'yan jarida 50 na farko da suka mika takardunsu. Amma kuma ba dan jaridar Turkiyyar ko daya daga cikinsu.

Ita dai Beate Zschaepe da sauran abokan huldarta su hudu ana zargin su ne da kasancewa mambobin kungiyar masu raya manufofin NAZI wato NSU da suka halaka mutane 10 dukansu baki a Jamus ciki har da da 'yan Turkiya 8 da kuma wani dan Girka.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Mouhamadou Awal Balarabe