1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Turkiya na ci gaba da kamen malaman jami'o'i

Gazali Abdou TasawaAugust 19, 2016

Turkiya ta bada sammacin kamo wasu malaman jami'o'i 146 a bisa zargin kasancewarsu masu alaka da Fethulla Gülen wanda mahukuntan Turkiyar ke zargi da kitsa juyin mulkin da ya ci tura.

https://p.dw.com/p/1JlmI
Türkei Mugla Verhaftungen nach Putschversuch
Hoto: picture-alliance/Zuma/T. Adanali

Wannan mataki ya shafi malaman jami'ar birnin Konya na tsakiyar kasar su 84 da na jami'ar birnin Istanbul 62.

Kamfanonin dillancin labarai na Anadolu da na Dogan na kasar ta turkiya sun ruwaito cewa yanzu haka ana tsare da 44 daga cikin malaman a cikin harabar jami'ar Istanbul , da wasu 29 a jami'ar birnin na Konya a ci gaba da aikin kamen da mahukuntar kasar suka kaddamar a cikin jihohi 17 na kasar.

Jami'an 'yan sanda sun kuma gudanar da bincike a ofisoshi dama a gidajen iyalan malaman jami'ar da ake zargi da hannun a cikin juyin mulkin da bai yi nasara ba

Ma'aikata sama da dubu biyar ne aka kora daga aiki a yayin da aka dakatar da aikin wasu dubu 80 ,kana ake tsare da wasu mutanen dubu 20 tun bayan soma wannan aiki na kamen da ya biyo bayan yunkurin juyin mulkin da ya ci tura a kasar ta Turkiya.