1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tunawa da kisan kiyashi ga Yahudawa a Turai

January 27, 2013

A yau ne a fadin kasar Jamus ake zaman tunawa da wadanda ta'asar kisan kiyashi da 'yan Nazi suka aikata ta shafa.

https://p.dw.com/p/17SEM
Ukrainian Jews stand in front of the Minora monument during a mourning ceremony near the ravine Babiy Yar in Kiev, 23 September 2007. Ukrainians commemorated the 66th anniversary of the Nazi massacre of Jews at Babiy Yar ravine in Kiev where some 34 000 Jews were murdered during two days 29 and 30 September 1941. In total more than 100 000 people lost their lives in Babiy Yar between 1941 and 1943. EPA/SERGEY DOLZHENKO +++(c) dpa - Bildfunk+++
Hoto: picture-alliance/dpa

Majalisun dokokin da kungiyoyi za su yi zama a sansanonin kisan kiyashin domin tunawa da tsangwama da kuma kisan da Yahudwa suka fuskanta a fadin nahiyar Turai. Shugabar gwamnatin Jamus, Angela Merkel a cikin jawabin da ta yi ta hanyar bidiyo ta nananta cewa Jamusawa sune ke da alhakin taasar da da yan Nazi suka aikata. A ranar 27 ga watan Janairun kowace shekara ne dai ake tunawa da wannan rana kasancewar a ranar 27 ga watan Janairun shekarar 1945 ne dakarun Rasha suka yantar da yahudawa a sansanonin da ake azabatar da su a garin Auschwitz dake kasar Poland. Shi dai sansanin na Auschwitz na zamam alamar tunawa da kisan kiyashi da aka yi wa miliyoyin jamaa a lokacin mulkin yan Nazi.

Mawallafiya: Halima Balaraba Abbas
Edita: Saleh Umar Saleh