Tana kasa tana dabo kan zaman lafiyar Sudan ta Kudu
March 6, 2020Bari mu fara da jaridar Die Tageszeitung da ta yi sharhi kan kasar Sudan ta Kudu tana mai cewa: Ba sauki ba ne ka samu 'yan Sudan ta Kudu da ke da kwarin gwiwa a kan sabuwar gwamnatin rikon kwarya da masu adawa da juna wato shugaban kasa Salva Kiir da mataimakin shugaba kuma madugun 'yan tawaye, Riek Machar suke wa jagora da ke da burin kawo zaman lafiya a kasar. A karshen watan Fabrairu ne aka shigar da Machar da wasu shugabannin adawa cikin sabuwar gwamnatin hadin kan kasa. Matakin da Shugaba Kiir ya ce ya kawo karshen yakin kusan shekaru bakwai, sai dai har yanzu bangarorin ba su kai ga amincewa da raba mukaman ministoci ba, lamarin da masharhanta ke bayyana shi da cewa ka iya sa a koma gidan jiya. Hasali ma akwai wasu kungiyoyin 'yan tawayen da suka yi barazana ci gaba da tada kayar baya.
Kasar Jibuti da ke yankin kahon Afirka ta kirkiro da sabon tsarin kasuwanci mai ban sha'awa, inji jaridar Süddeutsche Zeitung. Ta ce karamar kasar dai tana ba da hayar wasu filayenta ga dakarun kasashen ketare da ke gina sansanonin sojojinsu. Komai na tafiya da kyau, yanzu haka kuma kasashen Faransa da Birtaniya da Amirka da Italiya da Spain da Jamus sun kafa sansanonin sojinsu a Jibutin, yayin da sansanin sojin kasar Japan jiragen ruwan Koriya ta Kudu ne ke isa. Chaina ta zama kasa ta baya bayan nan da ta kafa sansanin sojinta a yayin da Indiya da Saudiyya suka nunar sha'awar bin sahu. Jaridar ta ce wannan wata matattarar kasashe ne da bisa al'ada suke adawa da juna. Tuni ma Chaina ke zargin jiragen saman Amirka da yin shawagi kusa da sansaninta don yi mata leken asiri. Ita kuma Amirka na zargin kasar ta Sin da daukar hotunan sansaninta a boye. Jaridar ta saka ayar tambaya ko za a kare lafiya kuwa a dan karamin wurin da ya hada sojojin daga kasashen da ke nuna wa juna 'yar yatsa?
Ita kuwa jaridar Neue Zürcher Zeitung a wannan mako cewa ta yi ana kara nuna damuwa a Afirka. Ta ce ga kasashen Afirka Kudu da Sahara cutar Coronavirus na zama wani kalubale na musamman. Ta ce bullar cutar a wasu kasashen Afirka ta sanya fargaba a zukatan mutane miliyan dubu 1.3 a nahiyar. Sai dai abin da ya fi jan hankali shi ne da ma akwai wasu cututtuka, amma saboda rashin kyakkyawan tsarin kiwon lafiya a mafi akasarin kasashen Afirka, ba a gane su ba. Jaridar ta ce abin tsoro a nan shi ne cutar ta Corona ka iya yaduwa cikin sauri a nahiyar inda kuma za ta iya yin mummunar illa. Saboda kyakkyawar huldar kasuwanci tsakanin Chaina da yawancin kasashen Afirka, inda aka kiyasta Chaina na da kamfanoni kimanin dubu 10, tuni Covid-19 ta janyo matsalolin tattalin arziki.