1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsugune ba ta kare ba a PDP

Usman ShehuDecember 5, 2013

Shugabannin PDP za su je kotu don hukunta gwamnoni biyar da suka juyawa jam'iyyar baya kana suka shiga APC mai adawa

https://p.dw.com/p/1AT9z
Hoto: DW/T. Mösch

Akalla manyan lauyoyin kasar 12 ne dai PDP ta ce ta dauka da nufin nazarin rikicin tare da tunkarar kotu idan hali ya yi. A wani abun da ke zaman alamar baya da kura a cikin rikicin da sannu a hankali ke sauyin launi da salo sannan kuma ke barazana ga makomar jamiyyar, da ta share shekaru dayawa ta na cin karenta babu babbaka.

Duk da cewar dai jam'iyyar ba ta kai ga sa rana ko kuma ambato yawan 'yan tawayen da take tunanin gurfanarwa, da nufin raba su da kujerun alfarmar cikin kasar ta Najeriya ba dai, tuni sabon matsayin ya fara dagun hakarkari. Kama daga masu adawar APC da suke murnar samun garabasar ta bana ya zuwa 'yan kallo na siyasar da ke ganin rikidar ta cikin yanayi na kankanewa.

Aliyu Magatakarda Wamakko Gouverneur von Sokoto Nigeria
Gwamnan Sokoto Aliyu Magatakarda WamakkoHoto: DW/T. Mösch

PDP dai na fatan barazana ta kaiwa kotun na iya kai tsoro ya zuwa zaurukan majalisun kasar biyu, in da shiri ya yi nisa na rikidar yan dokar zuwa ga dandali na adawa. Abun kuma da ka iya kaiwa ga kammala sauyi na siyasar tare da tabbatar da kare babakeren PDP mai mulki. To sai dai kuma a fadar Buba Galadima da ke zaman jigo a cikin APC wai tuni mushen kura ya dai na baiwa yaran na adawa tsoro.

Aikata laifi na barin PDP ko kuma kokari na lahanta giwa ta siyasa dai, babban kuskure ne a bangaren PDP da take kokarin gyarawa yanzu a cewar Ahmed Ali Gulak da ke baiwa shugaban kasar shawara ta siyasa. Kokarin karbar baki da sauya musu launi domin buri na siyasa.

Plakat Nigeria Präsidentenwahlkampf
Bamanga Tukur shugaban PDPHoto: DW/U.Haussa

Gyaran kama karya ko kuma kokari na bude ido a cikin sauyi maras dadi dai, an sha sauyin sheka ciki dama wajen jam'iyyun kasar ta Najeriya ba tare da kaiwa ga dagun hakarkari, ba balle asara ta kujera.

To sai dai kuma kundin tsarin mulkin a fadar Barister Sani Hussaini Garun Gabas, da ke zaman wani lauya mai zaman kansa cikin kasar ya kai ga jerin tanadi na hukuncin laifukan da ke da ruwa da tsaki da kokarin sauyin shekar.

Abun jira a gani dai na zaman mataki na gaba a cikin jam'iyyar da ke kokari na kakkabe kowa da nufin tunkarar zabukan kasar na shekara ta 2015 da sauran karfi a jika.

Mawallafi: Ubale Musa

Edita: Usman Shehu Usman

Tsallake zuwa bangare na gaba Bincika karin bayani

Bincika karin bayani