1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsokacin kungiyoyi kan dangantakar Faransa da Chadi

Wackernagel Tamara/ S.BabayoMarch 4, 2016

Yayin da ake shirin zaben shugaban kasa a Chadi, kungiyoyin fararen hula na kara matsin lamba na ganin gwamnatin Faransa ta daina hada kai da Shugaba Idriss Deby.

https://p.dw.com/p/1I7Ms
Tschad N'djamena Saleh Kebzabo (L) and Ngarlejy Yorongar
'Yan adawan kasar Chadi Saleh Kebzabo da Ngarlejy YorongarHoto: Getty Images/AFP/G. Cogne

Makonni shida suka rage a gudanar da zaben shugaba kasa, inda Shugaba Idriss Deby na kasar ta Chadi da ke yankin tsakiyar Afirka zai fafata da wasu 'yan takara masu yawa. Kotun tsarin mulkin kasar ta yi watsi da takaran mutane tara daga cikin 23, abin da ya janyo yanzu ake da 'yan takara 14 wadanda za su tankari shugaban

Matsin lambar kungiyoyin a kasar Chadi

Sai dai kungiyoyin fararen hula suna kara matsin lamba na ganin Faransa ta daina tallafa wa shugabannin da suke kama karya na Afirka, musamman kasashen da Faransa ta yi wa mulkin mallaka kamar Chadi. Kungiyoyin sun kara tashi tsaye bayan zanga-zangar da aka yi a Chadi lokacin da wasu suka ci zarafin wata 'yan mata 'yar shekaru 17 da ake kira Zouhoura, da kuma yadda suke ganin kasar tana sukurkucewa, inda suke caccakar Shugaba Deby da Faransa da ke mara masa baya. Juliette Poirson take magana da yawun wata kungiyar kare rayuwa wadda ta dangata matsalar Chadi da hadin kan da Shubana kasar ke samu daga Faransa ta yi tsokaci:

Tschad Zouhoura Protest
Hadin gwiwar kungiyoyi masu zanga-zanga a ChadiHoto: DW/B.Dariustone

"Akwai hadin kai na sojoji, abin da ya shafi doka, wanda babu mutunta hakkin dan Adam, rawar da bai kamata ba. Mu kungiyarmu tana neman kulla hadaka na soji da tsaro, da daukar nauyin samar da matakan da ake bukata."

Kungoyoyin su na sukar dangantakar ne saboda rashin mutunta hakkin dan Adam. Faransa tana taimakon Chadi saboda yaki da ta'addanci da tashe-tahsen hankula. Amma Antoine Glasser ya kara da cewa ba lalle ba ne haka ya kasance shi ne ya janyo abubuwan da ke faruwa a kasar ta Chadi ba:

Tschad Präsident Idriss Déby Itno
Shugaba Idriss Déby Itno lokacin da jam'iyyarsa ta kaddamar da shi a zabe mai zuwaHoto: DW/B. Dariustone

Zargi kan hade baki tsakanin Deby da kasar Faransa

"An bai wa Faransa karfi fiye da kima, gaskiya ce suna da karfi, a wurare kamar Chadi. Amma idan al'uma ta tashi tsaye dole Deby ya tafi, ko Faransa ba ta isa ta kare shi ba. Wannan shi ne karon farko da kungiyoyi masu zaman kansu suka tashi tsaye suka janyo wani tasiri kan siyasar kasar da yajin aikin gama gari kuma yana da muhimmanci."

Sai dai abubuwan da suke faruwa zai yi wuya su sauya yadda sakamakon zaben shugaban kasa na Chadi wanda za a yi nan da makonni shida masu zuwa zai kasance.