1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsohon shugaban Brazil ya ki mika kai ga 'yan sanda

Gazali Abdou Tasawa
April 7, 2018

Tsohon Shuban Brazil Luiz Inacio Lula da Silva wanda kotu ta same shi da aikata laifin cin hanci, ya bijire wa umurnin hukumar shari'a na kai kansa ofishin 'yan sanda na birnin Curitiba

https://p.dw.com/p/2vdft
Luiz Inacio Lula da Silva
Hoto: picture-alliance/AP Photo/E. Peres

Tsohon Shuban kasar Brazil Luiz Inacio Lula da Silva, wanda kotun kasar ta ba da umurnin kargame shi a gidan kurkuku bayan da ta same shi da aikata laifin karbar cin hanci, ya bijire wa umurnin hukumar shari'a ta kasar na kai kansa ofishin 'yan sanda na birnin Curitiba da ke kudancin kasar. Yanzu haka tsohon shugaban kasar ta Brazil mai shekaru 72 nan can ya buya a babbar cibiyar kwadago ta birnin Sao Polo, inda dubban magoya bayansa suka taru domin neman su hana a kama shi.

Kotun kasar ta Brazil dai ta yanke wa tsohon shugaban hukuncin zaman wakafi na shekaru 12, sakamakon samun sa da aikata laifin karbar rashawa. Sai dai yanzu haka lauyoyinsa na tattauna wa da 'yan sanda domin samun damar sake daukaka kara. Tsohon Shugaba Lula na Brazil na da burin sake tsayawa takara ne a zaben shugaban kasar da ke tafe, inda kuma masu lura da harakokin siyasar kasar ke cewa zai iya lashe zaben, kasancewa a yanzu haka yana da farin jini sosai a kasar.