Tsayawar Jonathan a zaɓen baɗi
June 20, 2010Shugaban Najeriya Goodluck Jonathan ya bayyana cewa lokaci bai yi ba, da zai yanke shawara walau ko zai tsaya takarar shugaban ƙasar a zaɓen baɗi. A wata hirar da aka watsa ta gidan talavijin mallakar gwamnatin ƙasar wato NTA, Jonathan ya ce yanzu zai kasance gaggawa, idan ya ce zai tsaya ko a'a. A ƙasar dai ana bayyana cewa akwai matakai da yawa dake nuna alamun Jonathan na kimtsawa shiga takarar shugabancin ƙasar, abinda zai ba shi damar zarcewa.
A wani abinda ya shafi Tarayyar ta Najeriya, ƙungiyar ƙwallon ƙafan ƙasar ta Super Eagle, ta buƙaci gwamnatin ƙasar da ta samarwa ɗan wasan ƙasar Sani Kaita tsaro, domin a faɗar ƙungiyar tun lokacin da aka baiwa Sani Kaita jan kati a wasansu da Denmark, Sanin ya samu saƙwannin tawaya kimanin 1000, dake barazanar hallaka shi, bisa tsautsayin da ya haddasa ba shi katin, inda wasu ke ganin haka ya sa Najeriya ta sha kashi a hannun Denmark.
Mawallafi: Usman Shehu Usman
Edita: Mohammed Nasiru Awal