1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsamin dangantaka tsakanin Rasha da Amirka

August 8, 2013

Soke ganawa tsakanin Barack Obama da Vladimir Putin na nufin kara tsuke dangantaka dake da rauni tun zamanin cacar baka tsakanin Mosko da Washington.

https://p.dw.com/p/19Mey
U.S. President Barack Obama (R) meets with Russia's President Vladimir Putin in Los Cabos, Mexico, June 18, 2012. The leaders are in Los Cabos to attend the G20 summit. REUTERS/Jason Reed (MEXICO - Tags: POLITICS)
Hoto: Reuters

Kwararru da masana harkokin siyasa na ci gaba da tsokaci dangane da soke tattaunawa da shugaban Rasha da Barack Obama na Amirka ya yi. Abun da a cewarsu zai kara lalata dangantakar kasashen biyu da tuni yake da rauni. Hakan dai yana da nasaba ne da mafakar siyasa na wucin gadi da Rashan ta ba wa tsohon jami'in hukumar leken asirin Amirka Edward Snowden.

Soke wannan ganawa tsakanin Barack Obama da Vladimir Putin dai, na nufin kara tsuke dangantaka dake da rauni tun zamanin cacar baka tsakaninsu. Batu da ake ganin zai iya haifar wa Putin suka a fadar gwamnati ta Kremlin. Tafiyar Obama zuwa Saint Petersburg domin halartar taron kungiyar kasashe masu ci-gaban masana'antu na G20 dai yana nan kamar yadda aka tsara, taron da Rashan za ta kasance mai masaukin baki, sai dai ba zai yada zango a Mosko domin tattaunawa da Putin ba, kamar yadda yake tun da farko.

Country leaders (L-R) Russia's President Vladimir Putin, Britain's Prime Minister David Cameron and U.S. President Barack Obama attend a working session at the Lough Erne golf resort where the G8 summit is taking place in Enniskillen, Northern Ireland June 18, 2013. REUTERS/Yves Herman (NORTHERN IRELAND - Tags: POLITICS)
Putin, da Cameron da kuma Obama a taron G8Hoto: Reuters

Lokaci mawuyaci tsakanin Washington da Mosko

A cewar masani kan harkokin siyasa dake cibiyar Carnegie dake Mosko Lilya Shevtsova, akwai alamun dake tabbatar da cewar, dangantaka tsakanin Washinton da Mosko tana kara yin tsami. Akwai tambayoyi da yawa da bangarorin biyu ba za su iya cimma nasarar kusantar amsasu ba.

Sai dai a bangaren daya Matthew Rojanski dake cibiyar Kennen a Washington ya ce wannan babban kuskure ne a bangaren Obama.

"Wannan kuskure yayi na furta wannan sanarwar soke tattaunawar tasu kafin ganawar da za ta gudana tsakanin sakatarorin harkokin wajen kasashen biyu a ranar Juma'a, wanda ke tabbatar da cewar ganawar ba za ta haifar da komai ba. Kazalika ba za a cimma warware wannan matsalar nan da watan Satumba ba."

Amurka dai ta soke ganawar magabatan biyu ne, mako guda bayan da gwamnatin Rashan ta ba wa tsohon jami'in hukumar leken asirin Amirka Edward Snowden mafaka ta siyasa, mutumin da Washington ke neman shi ruwa a jallo domin ya fuskanci shari'a, saboda yin tonon silili kan shirin Amirka na tatsar wasu bayanan sirri a asirce.

Soke tattaunawar zai shafi harkokin siyasa

To sai dai majiyar fadar gwamnatin Rasha ta Kremlin ta ce Amirkan ta fake ne kadai da wannan batu na Snowden, domin soke ziyarar. Zance na gaskiya shi ne, Amirkawa na guje wa tattaunawar keke da keke ne tsakanin bangarorin biyu, wanda hakan ko shakka babu zai shafi lamuran siyasa.

epa03809713 (FILE) A file video grab courtesy of British The Guardian newspaper, London 10 June 2013 showing former CIA employee Edward Snowden during an exclusive interview with the newspaper's Glenn Greenwald and Laura Poitras in Hong kong. Media reports on 01 August 2013 state that US whistleblower Edward Snowden has left Moscow airport after he has been granted temporary asylum in Russia in a statement by his lawyer. EPA/GLENN GREENWALD / LAURA POITRAS / HANDOUT MANDATORY CREDIT: GUARDIAN / GLENN GREENWALD / LAURA POITRAS, HANDOUT EDITORIAL USE ONLY/NO SALES
Edward Snowden tsohon jami'in leken asirin AmirkaHoto: picture-alliance/dpa

A cewar kwararre Mathew dai, Amirka ta yi azarbabi wajen daukar wannan mataki...

"Duk da cewar Rasha ba ta bayar da hadin kan da fadar gwamnatin Amirka ta White House ke muradi, hakan ba ya nufin cewar ba za a fidda tsammanin samun hadin kanta ba. Rasha abokiyar shawararmu ce, wasu daga cikin abubuwan da za ka ji wasu 'yan siyasa na fadi shi ne, mu soke halartar wasannin motsa jiki na Olympics da za a yi a kasar. Wadannan duk matakai ne da ba su cancanta a dauka ba, musamman ma a lokaci mawuyaci kamar wannan."

Kwararre a kan lamuran siyasa na Rasha Dmitri Trenin a wani sharhi da ya yi ta yanar gizo, ya nunar da cewar soke tataunawa tsakanin Obama da Putin zai iya daukar wata alkibla. Obama da wasu kasashen yammaci za su iya kaurace wa wasannin Olympics da za ayi a Rasha a 2014. Kazalika zai dasa aya a kan taron kasashe masu ci-gaban masana'antu na G8 da kasar za ta kasance mai masaukin baki a shekara mai zuwa.

Mawallafa: Roman Goncharenko / Zainab Mohammed Abubakar
Edita: Mohammad Nasiru Awal