Tsamin dangantaka tsakanin Putin da Erdogan
November 27, 2015Talla
Ministan harkokin wajen Rasha din Sergey Lavrov ya ce sun yanke shawarar yin hakan be saboda Turkiyya ta zama wata kasa da 'yan ta'adda ke amfani da ita wajen isa ga abokan burminsu kana ta ki amicewa ta yi musayar bayanai na sirri da Rasha dangane da 'yan kasar ta Rasha da ake zargi da alaka da kungiyoyin 'yan ta'adda.
Rasha dai ta ce wannan sabon tsarin zai fara aiki daga farkon watan Janairun shekarar da muke shirin shiga. Wannan na zuwa ne daidai lokacin da zaman tankiya ke cigaba da karuwa tsakanin kasashen biyu tun bayan da Turkiyya ta harbo jirgin yakin Rasha bisa zargin keta sararin samaniyarta ba tare da izini ba.