1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tsagaita wuta tsakanin masu fafatawa a Gaza

Yusuf Bala Nayaya MNA
May 6, 2019

Shugabannin Falasdinawa a yankin Gaza sun amince da shirin tsagaita bude wuta tsakaninsu da Isra'ila a wannan Litinin, don kawo karshen lugudan wuta da ake tsakanin bangarorin biyu a tsawon kwanaki biyu.

https://p.dw.com/p/3HyW5
Gaza-City Zerstörungen nach Luftangriffen aus Israel
Hoto: Reuters/S. Salem

Lugudan wutar da aka fara dai ka iya rikidewa zuwa yaki tsakanin Isra'ila da Falasdinawan kamar yadda wadanda ke kusa da kulla yarjejeniyar dakatar da bude wutar suka bayyana.

Daga bangaren dakarun na Isra'ila mai magana da yawun sojojin taki cewa komai game da batun yarjejeniyar da Masar ta shiga tsakani aka kulla, kamar yadda wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa na AFP ya bayyana. Wani jami'i daga Masar ma da bai so a bayyana sunanasa ba ya bayyana batun yarjejeniyar, haka nan wasu rahotanni da ke fitowa sun nunar da cewa an fara janye wasu shingayen da Isra'ila ta kafa bayan da fadan ya fara kazanta.

Gumurzun fadan dai ya girmama ne tun a ranar Asabar bayan da aka harba makaman roka daga yankin na Gaza zuwa Isra'ila, ita kuwa Isra'ila ta mayar da zafafan hare-hare da suka yi sanadi na rayukan Falasdinawa 23, yayin da daga bangaren na Isara'ila aka rasa rayuka hudu.