1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ɓangarorin da ke yaƘar juna a Yemen za su tsagaita wuta

Lateefa Mustapha Ja'afarJuly 10, 2015

Kungiyoyin da ke yaƘar juna a Ƙasar Yemen sun amince da yarjejeniyar tsagaita wuta a dai-dai lokacin da azumin watan Ramadana ke daf da kawo ƙarshe.

https://p.dw.com/p/1Fwcz
Hoto: picture-alliance/dpa/Y. Arhab

Majalisar Ɗinkin Duniya ce dai ta buƙaci hakan daga ɓangarorin biyu domin samun damar isar da kayan agaji ga al'ummar ƙasar da yaƙi ya tagayyara. Sai dai duk da shiga tsakanin da Majalisar Ɗinkin Duniya ta yi har aka kai ga cimma wannan yarjejeniya, rahotanni sun nunar da cewar jiragen yaƙin rundunar taron dangi da Saudiyya ke wa jagoranci sun yi luguden wuta cikin dare a ƙasar yayin da a hannu guda kuma aka gwabza fada ta ƙasa tsakanin ɓangarorin biyu. Yarjejeniyar tsagaita wutar da ɓangarorin suka cimma dai ta tsahon mako guda za ta zo karshe ne a dai-dai lokacin da al'ummar musulmi a faɗin duniya ke kammala azumin watan Ramadana na bana. Dubun-dubatar al'ummar ƙasar ta Yemen ne dai suka shiga halin tasku yayin da wasu da dama suka hallaka tun bayan da rundunar taron dangin da Saudiya ke jagorantar ta fara kai hare-harenta cikin watan Maris din da ya gabata.