Trump ya yi amai ya lashe kan Rasha
July 18, 2018Talla
A wani yunkuri na kwaskware subutar baki a yayin ganawarsa ta musamman da shugaban Rasha Vladimir Putin a birnin Helsinki na kasar Finlan, Shugaba Donald Trump Amirka ya ce kuskure ne a kalamansa na farko da ya fifita Rasha a kan hukumar tattara bayanan sirrin Amirka na zargin taimaka wa Trump a kan Hillary Clinton a zaben shekarar 2016.
Trump ya lashe aman da ya yi ne kwana guda bayan da ya sha suka daga 'yan majalisar Amirka ciki har da 'yan jam'iyyarsa ta Republican da suka bukace shi ya sauya matsayinsa cikin gaggawa.