1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump ya san halin da Kim Jong Un ke ciki

April 28, 2020

Shugaban Amirka Donald Trump ya ce yana da masaniyar halin da  Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa ke ciki

https://p.dw.com/p/3bVDH
USA | Nordkorea | Entmilitarisierte Zone | Donald Trump | Kim Jong Un
Hoto: AFP/Getty Images/B. Smialowski

Wannan na nufin ke nan Trump ya tabbatar cewa Kim Jong Un yana nan a raye bai mutu ba kamar yadda ake ta jita-jita a kai.


A wurin taron 'yan jarida da Trump ya saba yi a fadarsa ta White House ya ce yana fata shugaban na Koriya ta Arewa na cikin koshin lafiya amma dai ba zai tsawaita bayani a kan halin Kim Jong Un ba saboda yanzu lokaci bai yi ba amma nan gaba kadan duniya za ta san halin da ya ke ciki.


An dai kwashe kwanaki ana ta rade-radin mutuwar Kim Jong Un tun  ranar 11 ga watan Afrilu lokacin da aka daina ganinsa a bainar jama'a.