1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Trump da Putin sun kawo karshen gaba tsakaninsu

Binta Aliyu Zurmi AH
July 16, 2018

Shugabannin biyu sun hadu a birnin Helsinki na kasar Finland inda suka tattauna batutuwan da ke haddasa sabani tsakanin Amirka da Rasha.

https://p.dw.com/p/31YjQ
Helsinki Trump-Putin Gipfel
Hoto: Reuters/K. Lamarque

Rashin jituwa tsakanin Amirka da Rasha na tsawon lokaci ya sa ganawar musamman tsakanin shugabannin kasashen biyu ya dauki hankalin duniya. Shugaba Trump da takwaransa na Rasha Mr. Putin, sun yi watsi da duk wasu bambance-bambance da ke tsakanin kasashensu don samun fahimtar juna. A yayin jawabinsa, Shugaba Trump ya nuna alamun lamura sun sauya a 'yan sa'oin da suka gana da Shugaba Putin inda ya ce: " Ganawarmu yana da muhimmanci, kuma mun fara shi a da kafar dama."

Finnland Helsinki PK Treffen Trump Putin
Shugaban Amirka Donald TrumpHoto: Reuters/G. Dukor
Finnland Helsinki PK Treffen Trump Putin
Shugaban Rasha Vladimir PutunHoto: Reuters/G. Dukor

Wannan ita ce ganawa ta farko da shugabannin  biyu suka yi na musamman, tun bayan cece-kuce da ya biyo baya zargin da ake wa Rasha na taka rawa a rikicin kasashen Ukraine da Siriya, da ma zargin yin kutse a zaben Amirka na shekarar 2016. Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya ce: "Ina tunanin yau Trump zai sami irin bayanin da zai kara gamsar da shi kan halin da ake ciki, shakka babu an sami sauyi amma kuma ina fatan ganin kwakwaran sauyi nan gaba''

Taron shugabannin biyu a birnin Helsinki na kasar Finlan ya gudana cikin matakan tsaro, amman wannan bai hana wasu 'yan kasar Rasha da ke zaune a birnin gudanar da zanga-zanga ba. A baya dai Amirka ta yi karin takunkumi ga kasar Rasha, tare da korar wasu jami'an diflomasiyyar kasar daga Amirka, matakin da Rasha ta mayar da martanin sallamar jami'an Amirka daga kasar ta.