1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An watse baram-baram a ganawar Trump da Kim Jong Un

Abdourahamane Hassane
February 28, 2019

An watse daga zaman taron samar da mafita kan batun jingine shirin nukilya a tsakanin Shugaba Donald Trump na Amirka da takwaransa na Koriya ta Arewa Kim Jong Un ba tare da an cimma nasara ba,

https://p.dw.com/p/3EHAf
Vietnam l Hanoi, US-Präsident Donald Trump trifft den nordkoreanischen Staatschef Kim Jong Un
Hoto: Reuters/L. Millis

Taron wanda shi ne irinsa na biyu da shugabanin biyu ke yi, Shugaba Trump da takwaransa KiM Jong Un suna nuna alamu na samun fahimta , sai dai bayan kwashe sa'oi ana tattaunawa da ake ganin tamkar sabon babi na tarihi ne ake shirin budewa, sai shugabanin suka fito da bayanai marasa dadi, babu yarjejeniyar da suka kulla a takaice  babu wani ci gaba a zaman taron na yini biyu da ya gudana a birnin Hanoi, a jawabinsa gaban manema labarai Shugaba Trump ya ce ba a cimma nasara ba amma hakan baya nufin babu sauran dama nan gaba. Babu dai bayani daga bakin Shugaba Kim bayan da aka tashi daga zaman amma kuma wani masani kuma farfesa na jami'ar Donggkuk da ke Koriya ta Arewa,  mai bibiyan lamuran kasa da kasa Mista Koh Yu-Hwan, ya ce sam Shugaba Kim bai yi azanci ba don kuwa batu ne da zai sa janyo masa suka.