Togo ta cire wa Agbéyomé Kodjo rigar kariya
March 16, 2020Majalisar dokokin kasar Togo ta cire rigar kariya ta dan adawa Agbéyomé Kodjo - wanda ya zo na biyu a zaben shugaban kasa na 22 ga watan Fabrairu - bisa bukatar kotu da ke son gurfanar da shi a gaban kuliya bisa zargi kan tsaron kasa. 'Yan majalisa 80 sun kada kuri'ar amincewa da matakin, yayin da wakilai biyu suka kada kuri'un kin cire rigar kariyar, sannan takwas suka yi rowar kuri'arsu. Sai sai Mista Kodjo wanda abin ya shafa bai halarci zauren majalisar ba.
Cikin wata wasika da ya aika a makon da ya gabata, babban mai gabatar da kara na kasa Essolissam Poyodi ya zargi dan adawan da ayyanan kansa a matsayin shugaban kasa, lamarin da ya saba wa dokokin Togo. Shi dai Agbéyomé Kodjo ya samu kashi kusan 20% na kuri’un da aka kada, yayin da shugaban mai barin gado Faure Gnassingbé ya samu kashi sama da 70%. Sai dan adawan ya shigar da kara gaban kotun tsarin mulki kan zargin aringizon kuri'u, amma kotu ta yi watsi da karar.