Faure Gnassingbe ya sake lashe zaben shugaban kasa
March 3, 2020Shugaba mai ci na kasar Togo Faure Gnassingbe ya lashe babban zaben shugaban kasar da aka gudanar a makon jiya da kashi sabain da daya cikin dari. Gnassingbe zai ci gaba da jan ragamar mulkin kasar da ya soma shekaru goma sha biyar da suka bayan mahaifinsa.
Sanarwar sakamakon zaben da kotun ta yi, ta ce ya kawo karshen duk wani jan-in-ja da ya dabaibaye zaben na watan Febrairu. Kawo yanzu dai babu martani daga bangaren madugun adawa Gabriel Messan Agbeyome Kodjo da ya ce, jam'iyyarsa ce ta yi nasara da kashi sittin cikin dari na kuri'un da aka kada.
Shugaba Gnassingbe na da shekaru biyar a sabon wa'adin mulki. Tun dai daga shekara 2017 ne dai iyalan Gnassingbe suka soma fuskantar matsi daga bangaren adawa daga 'yan kasar da suka bukaci kawo karshen mulki da iyalan Gnassingbe suka kwashe shekaru 50 suna yi.