Tatsar bayanan sirri na 'yan adawa a Togo
August 5, 2020Talla
Kungiyoyin farar hular sun zargin gwamnatin da sanya ido a kan wayoyin salula na 'yan fafutuka da shugabannin addinai da kuma 'yan adawa wadanda ta ke gani sun zamar mata barazana.
Wani kamfani na kasar Isara'ila mai suna NSO Group ake zargi da yi wa gwamnatin ta Togo wannan aiki tare da wasu kasashe na duniya kamar yadda jaridar The Guardian ta Birtaniya ta ruwaito.
Shugaban jam'iyyar Togolese People's Party mai adawa Nathaniel Olympio ya ce Shugaba Faure Gnassingbe' ya wuce gona da iri, yana mai cewa gwamnati ta mayar da kayan aikin da ya kamata ta yaki ta'addanci da su zuwa wurin yakar abokan hamayya da 'yan fafutuka.