1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Togo: Majalisa tana shirin kawo sauyi a tsarin mulki

Salissou Boukari
September 13, 2017

Shugaban majalisar dokokin kasar Togo Dama Dramani, ya sanar cewa a ranar Juma'a ce za su soma tattauna batun kawo sauye-sauyen kundin tsarin mulkin da 'yan adawan kasar suka matsa lamba a kai.

https://p.dw.com/p/2juoL
Togo Wahl Oppositonsführer Jean-Pierre Fabre
Jean-Pierre Fabre madugun 'yan adawan kasar TogoHoto: Issouf Sanogo/AFP/Getty Images

Shugaban majalisar ta Togo ya ce suna cikin yanayi na gaggawa, don haka ala tilas za su rufe zaman majalisar da suke a ranar Alhamis, domin a ranar Juma'a su dukufa kan ayoyin dokar da gwamnati ta aike musu musamman ma kan batun kayyade wa'adin mulki na shugaban kasa. Tuni dai aka bai wa kwamiti-kwamiti da rukuni-rukuni na 'yan majalisar takardun domin su yi nazari a kan su kafin su fitar da rahoton karshe wanda 'yan majalisar za su kada kuri'a a kanshi.

A ranar Litinin da ta gabata ce dai magatakardan majalisar dokokin ta Togo ya yi wani furuci ta gidan talbijin na kasar, inda ya ce daukan mataki na gaggawa wajen kawo sauyi a kundin tsarin mulki abu ne da doka ta haramta, sai dai kuma bisa dukkan alamu bangaran na gwamnati ba shi da wani zabi a halin yanzu ganin yadda boren 'yan adawan ke dada daukan sabon salo.