1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

An zabi shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu shugaban ECOWAS

Abdoulaye Mamane Amadou Suleiman Babayo
July 10, 2023

Sabon shugaban kungiyar bunkasa tattalin arzikin yammacin Afirka "ECOWAS" ya ce tsarin dimukuradiyya shi ne tafarkin jagoranci mafi inganci, duk da tarin kalubalen da ke tattare da shi.

https://p.dw.com/p/4TeGn
Standbild Video | Tinubu: 'We anchor well under President-elect Bola Ahmed Tinubu
Hoto: APTN

Shugaban Najeriya Bola Ahmed Tinubu da takwarorinsa suka zaba a matsayin sabon shugaban kungiyar ECOWAS a yayin taron kolinsu a jiya birnin Bisau Guine, ya kara da cewa yankin ba zai lamunta da juyin mulki cikin juyin mulki ba.

Shugaba Tinubu na kalamun ne a yayin da kasashe uku memebobin kungiyar da suka hada da Mali da Guinea Conakry da Burkina Faso ke karkashin jagorancin sojoji da suka kifar da gwamnatocin fararen hula shekararu ukun da suka gabata.

Kungiyar ECOWAS ta kuma kafa wani kwamitin nazari kan matakan tsaron da suka cancanta a Mali guda daga cikin mambobninta, tun bayan matakin janyewar rundunar Munisuma da ke aikin kiyaye zaman lafiya a wannan kasa.