1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taƙaitaccen tarihin Janar Muhammadu Buhari

Abdullahi Miadawa Kurgwi/ PAWMarch 26, 2015

Wannan ne karo na hudu da Janar din ke tsayawa takara, kuma ya samu karbuwa sosai wajen jama'a har ake mi shi lakabi da "mai gaskiya"

https://p.dw.com/p/1Exqd
Nigeria - nominierter Präsidentschaftskandidat Muhammadu Buhari
Hoto: Getty Images/P. Ekpei

An haifi Janar Muhammadu Buhari ranar 17 ga watan Disambar shekara ta 1942, kuma ya yi auren sa na fari ne tare da Safinatu, cikin shekarar 1971. Allah ya albarkaci auren da yara biyar, sai dai auren tasa da Safinatu, ya mutu a shekara ta 1988, sannan a watan Disambar 1989, Janar Buhari ya auri matar sa ta yanzu Aisha, wacce itama suka haifi 'ya'ya biyar.

Illimi da makarantun da ya je

Buhari ya faro karatunsa ne a makarantar Firamare na Mai'Adua da ke jihar Katsina, tsakanin shekarun 1948-52, kafin ya je makarantar nan ta Katsina Middle School 1953-55, sa'anan ya shiga makarantar sakandaren lardi ta Katsina Provincial, wanda yanzu ta koma kwalejin gomnati ta Katsina cikin 1956-1961. Daga nan ne kuma Buhari ya je makarantar horon soji da ke Kaduna, wanda aka fi sani da Nigerian Defence Academy ko kuma NDA yanzu, a shekarar 1961, sai kuma ya cigaba da samun horo ta fuskar aikin soji, inda harya sami damar samun karin illimi a wannan fanin, tsakanin 1962-1963 a kasar Ingila. Daga nan kuma ya je makarantar koyon dabarun aikin soji da ke Wellington India, tsakanin watan Janairu zuwa Nuwambar 1973, kafin kwalejin sanin dabarun yakki ta Amirka a 1979-1980.

Nigeria Oppositionsführer Muhammadu Buhari in Kano
Jama'a na mi shi taken "Sai mai gaskiya"Hoto: DW
Nigeria Bildergalerie Staatspräsidenten Muhammadu Buhari
Hoto: picture-alliance/AP Photo/A. Akinleye

Aiyyukan da Janar ya yi a gida Najeriya

A nan gida Najeriya, tsohon Janar din ya rike mukamai a aikin soji da dama, inda kuma ya zama gwamnan lardin arewa maso gabashin Najeriya cikin shekarar 1975, a zamanin gwamnatin Janar Murtala Mohammed. Janar Buhari ya zama shugaban kasa ne dai bayan wani juyin mulkin da sojoji suka yi wa gwamnatin Shehu Shagari, a ranar 31, ga watan Disambar shekarar 1983, inda kuma ya shugabanci kasar tsakanin shekarar 1984- 1985.

Gudunmawar da ya bayar ga kasa

Janar Buhari dai tarihi ya nuna irin gudummawar da ya bayar wajen kyautatuwar rayuwar jama'ar kasa, a fanonin da dama, mussamman ma lokacin da ya shugabanci asusun rarar man Fetur da marigayi Janar Sani Abacha ya kafa, inda al'ummar kasa ke yin kwatance da nasarorin da ya cimma a matsayin sa na shugaban wannan asusu da akafi sani da PTF.

Nigeria Oppositionsführer Muhammadu Buhari in Kano
Najeriya ta dade ba ta sami adawa haka baHoto: DW

Yawan lokutan da shugaban ya yi takara

Me yiwuwa don wannan kudiri na sa na samun daidaito cikin lamurar kasa ne ma ya sanya Janar Buhari neman shugabancin kasar a fagen mulkin Demokiradiyya, inda ya yi takarar neman shugabancin kasar a shekarar 2003 tare da tsohon shugaban Nigeriya Olusegun Obasanjo kana, a 2007 yayi takara da marigayi Umaru Musa yar'Adua, da kuma 2011, lokacin da suka fafata a zabe da shugaban kasa na yanzu Goodluck Jonathan, al'amarin da ke nuna cewa za'a kuma fafatawar a wannan karo tare da abokin karawar tasa a can baya, don haka ne ma duk inda yaje kamfe Janar Buhari kan yi yi jawabi tare da bayyana irin matsalolin da yake neman magance su idan ya sa mi shugabancin kasa.

Godiya ga masu ba da gudunmawa ga kamfe dinsa

Tsohon Janar din wanda ke da taken “ Sai mai gaskiya,” ya ce ba kudi ne da shi ba, da zai nemi takarar shugabancin kasa don haka ne ya bude asusun da yan Najeriya su kansu ke yin karo karo ciki, shi ne ma a ganawa da radiyon D W, Buhari ke yiwa jama'a godiya ta musamman don gudummawar su ga wannan asusu.