1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tawagar IAEA a Korea ta Arewa

June 27, 2007
https://p.dw.com/p/BuHp

Tawagar hukumar Majalisar Ɗinkin Dunia mai yaƙi da yaɗuwar makaman nuklea, ta kai ziyara gani da ido a ƙasar Korea ta Arewa.

Wannan tawaga, da Olli Heinonen ke jagoranta, ta bukaci gani a zahiri, tashar Yongbyon,inda Korea ta Arewa ke kera makamin nuklear.

Bayan yan sa´o´i na masanyar miyau, hukumomin Pyong Yang sun bada kai bori ya hau.

Kuma tun gobe a ka tsara tawagar zata ziyarci tashar Yongbyon da ke tazara kilomita 100 a arewancin Pyong yang babban birni.

Bayan taurin kann da su ka nuna, hukumomin Korea ta Arewa, a makon da ya gabata, su ka amince da ziyaratar wannan tasha, amma da sharaɗin su samu tallafin makamashi daga ƙasashe masu shiga tsakanin rikicin nulkear.

Wata sanarwar opishin tsaro na Pentagone, ta bayyana cewar, Amurika na shaku a game da binciken hukumar AIEA, a game da haka , Gwamnatin Amurika,ta bukacin sojojin ta, su gudanar da wani saban binciken, domin tabatar da gaskiyar rufe wannan tasha.