1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Ganawar Trump da Kim na tangal-tangal

Yusuf Bala Nayaya
May 23, 2018

A ranar 12 ga watan Yuni ne dai aka tsara ganawar shugabannin a kasar Singapor sai dai bayanan na Trump sun sake sanya shakku ko tattaunawar za ta yiwu.

https://p.dw.com/p/2yDRi
Bildkombo Kim Jong Un und Donald Trump
Hoto: picture-alliance/AP/dpa/Wong Maye-E

Shugaba  Donald Trump ya bayyana a wannan rana ta Laraba cewa sai a mako me zuwa ne zai sani ko tattaunawarsu da Shugaba Kim Jong Un na Koriya ta Arewa za ta faru ko kuwa a a: "Game da batun Singapor zamu ga yadda za ta wakana idan lokacin ya yi. Koma dai mene ne idan aka gana zai zama abu mai amfani ga Koriya ta Arewa."

A ranar 12 ga watan Yuni ne dai aka tsara ganawar shugabannin a kasar Singapor sai dai bayanan na Trump sun sake sanya shakku ko tattaunawar za ta yiwu.

Wasu dai jami'ai a fadar White House na shirin tafiya kasar ta Singapor a karshen wannan mako da ake sa rai za a yi tattaunawa me muhimmanci da Koriya ta Arewa kamar yadda wasu jami'an suka bayyana bisa sharudan ba za a bayyana sunansu ba.