1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Tattaunawar kafa gwamnati a Jamus

Yusuf Bala Nayaya
November 16, 2017

Shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta bayyana a wannan rana ta Alhamis cewa tana cike da fata na ganin an samu nasara a hadakar jam'iyyun da ake fatan za su kafa gwamnati a kasar.

https://p.dw.com/p/2nm1F
Deutschland Fortsetzung der Sondierungsgespräche
Hoto: picture alliance/dpa/K. Nietfeld

Shugabar gwamnatin ta bayyana haka ne a gabannin fara tattaunawa da wakilan jam'iyyarta ta CDU da 'yan kare manufofin kasuwanci Free Democrats da 'yan kare muhalli na Greens.

A cewar Merkel za ta yi nata bangaren na ganin yarjejeniyar mai lakabin Jamaika ta kai ga cimma gaci, ta kara da cewa sun tattauna kan batutuwa masu sarkakiya da aka ga nasara kamar batun sauyin yanayi da sufduri da batun 'yan gudun hijira.

Cikin dare ne dai wadannan wakilai za su zafafa muhawara kan sauran batrutuwa a kundin da suka shiga tattaunawar mai shafuka 61.