1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Yunkurin kawo karshen zubar da jini a Yemen

Lateefa Mustapha Ja'afarJune 1, 2015

Gwamnatin kasar Yemen da a yanzu haka shugaba da jami'anta ke gudun hijira ta sanar da cewa za a tattauna tsakanin 'yan tawayen Houthi na kasar da Amirka a Oman.

https://p.dw.com/p/1FZvV
Hare-haren Saudiya da kawayenta a Yemen
Hare-haren Saudiya da kawayenta a YemenHoto: picture-alliance/dpa/Y. Arhab

Wannan dai na zuwa ne a dai dai lokacin da ma'aikatar cikin gidan Amirka ta sanar da cewa akwai Amirkawa masu tarin yawa a hannun 'yan tawayen na Yemen wanda ta ce tana kokarin yin duk mai yiwuwa domin ganin an sako su.

A hannu guda kuma rundunar taron dangin da mahukuntan kasar Saudiya ke jagoranta na ci gaba da yin barin bama-bama a kan mayakan na Houthi, inda bayanai ke nuni da cewa daruruwan fararen hula ne suka rasa rayukansu mafiya yawa kananan yara tun bayan da Saudiya ta kaddamar da kai hare-hare a Yemen.