Rikicin tattalin arziki tsakanin Rasha da Amirka
August 10, 2018Talla
Mukaddashin firaministan Rasha din Dmitry Medvedev ne ya ambata hakan dazu inda ya ke cewar matakin da Amirka ke shirin dauka kan Rasha din zai shafi bankunanta da darajar kudin kasar wanda ba za su zuba idanu su bari hakan ta wakana ba.
Kalaman na Medvedev na zuwa ne daidai loakcin da shugaban Rasha din Vladmir Putin ya tattauna wannan batu da da majalisar tsaron kasar a fadarsa ta Kremlin, lamarin da ke nuna irin yadda Rashan ta dauki maganar da muhimmanci.