Nasarar yaki da 'yan bindiga a Zamfara
September 6, 2021Daukar matakin toshe layukan sadarwa da gwamnatin Nigeria ta yi a Jiihar Zamfara na da nufin dakile duk wata mu'amala tsakanin 'yan bindigar da masu basu bayanai.
A baya dai an sha zargin Jami'an tsaro akan rashin tabuka abin a zo a gani inda a wasu lokutan yi zargin cewa idan an kirasu basa zuwa zargin da suka sha musantawa.
Al'umma musamman mazauna yankunan karkara su ne hare-haren 'yan bindigar yafi shafa to ko za'a iya cewa sun fara ganin canji tun da aka fara daukar wadannan matakai?. Gwamnan Jihar Zamafara Alhaji Bello Matawalle yace kjwalliya ta fara biyan kudin sabulu.
Daukar matakin toshe layikan waya da gwamnatin jihar ta Zamfara ta yi shi ne karon farko a arewa maso yammacin Nigeria matakin da ake ganin sauran jihohi ka iya koyi da shi idan ya yi nasara.