1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaJamus

Miliyoyin 'yan Najeriya na fuskantar barazanar yunwa

Uwais Abubakar Idris RGB
May 15, 2023

Majalisar Dinkin Duniya ta nuna damuwa a kan karancin kudadden gudanarwa da ke fuskantar ayyukansu a Najeriya a sakamakon yake-yaken Sudan da Ukraine.

https://p.dw.com/p/4RN0U
Miliyoyin 'yan Najeriya na fuskantar barazanar yunwa in ji Majalisar Dinkin Duniya
Miliyoyin 'yan Najeriya na fuskantar barazanar yunwa in ji Majalisar Dinkin DuniyaHoto: Reuters/T. Ade

Wakilin Hukumar Kula da Ayyukan Jin kai ta Majalisar Dinkin Duniya a Najeriya ya nuna damuwa a kan karancin kudadden gudanarwa da ke fuskantar ayyukansu saboda illar da yake-yaken da ake fama da su a kasashen Sudan da Ukraine ke yi, wanda ya sanya raguwar samun kudadden, a daidai lokacin da ake fama da barazanar yunwa a Najeriyar da za ta shafi mutane miliyan 25 musamman mata da yara kanana. 

Najeriya na fuskantar barazanar yunwa
Najeriya na fuskantar barazanar yunwaHoto: picture-alliance/Zumapress/A. Lohr-Jones

Ayyukan Hukumar mai kula da jin kai ta Majalisar Dinkin duniya a Najeriya na ci gaba da fuskantar koma baya na raguwar abubuwan da suke yi a Najeriyar ne, tun bayan fara yaki na kasar Ukraine da ya dauki hankalin kasashen da ke taimaka wa kasar wajen bayar da tallafin na kula da kai dauki ga mutanen da ke hali na tagayara.

A yanzu da ake yaki a Sudan lamarin ya kama hanyara kara shiga mumunan hali, don wakilin hukumar a Najeriyar Mathias Scmale ya ce, daga cikin dala milyan 391 da suke bukata suna da dalla milyan 18 ne a hannu, abinda ya bar su a mumunan hali.

Rikicin Sudan ya lakume daruruwan rayuka
Rikicin Sudan ya lakume daruruwan rayukaHoto: Ahmed Satti/Anadolu Agency/picture alliance

Karancin abinci da barazanar da yunwa ke yi wa al'umma Najeriya ya sanya hukumomi a Najeriya tashi tsaye don wayar da kan al'umma a kan yadda yanayain noma na duke tsohon ciniki ke sauyawa a kasar.

Majalisar na aiki da gwamnatin Najeriya a kan wannan kalubale. Ana fatan kasashen da ke bayar da tallafi ba za su kau da kansu a kan Najeriyar ba domin barazanar yunwa ga alumma musamman mata da yara kananan, babban al’amari ne.