1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW
SiyasaArewacin Amurka

Tasirin zaben Amurka ga kasar Jamus

Christoph Hasselbach Zainab Mohammed Abubakar/SB
November 4, 2024

Ko shakka babu sakamakon zaben Amurka zai yi matukar tasiri ga Jamus, ba tare da la'akari da ko Kamala Harris ko kuma Donald Trump ne ya lashe zaben shugaban kasa a Amurka ba.

https://p.dw.com/p/4mb10
Hada hoton - Donald Trump da Kamala Harris
Donald Trump da Kamala HarrisHoto: AP/picture alliance

Lokacin da Joe Biden ya lashe zaben shugaban Amurka a 2020 bayan ya kayar da Donald Trump da ke mulki, mahukunta a Berlin sun nuna jin dadin sauyin da aka samu, saboda kallon Biden a matsayin dottijon dan siyasa, sabanin kallon rashin tabbas da ake wa Trump. Jam'iyyar ta Republikan na sake fita takara tare da mataimakiyar Shugaba Biden Kamala Harris a jam'iyyar Democrat. A bayyane take ita ce 'yar takarar gwamnatin Jamus, wacce ake fatan za ta ci gaba da kulla.

Karin Bayani: Harris da Trump na kace-nace a gangamin yakin neman zaben Amurka

Amurka | Kamala Harris | Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da Kamala Harris
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da Kamala HarrisHoto: SVEN HOPPE/AFP/Getty Images

Kaso biyu cikin uku na Jamusawa bisa ga binciken cibiyar Ipsos a farkon watan Oktoba, na son ganin Kamala Harris a matsayin shugabar Amurka, yayin da kaso 12 cikin 100 ne kawai ke goyon bayan Trump. Yaya girman tasirin sakamakon zaben ga Jamus?

Babbar ayar tambaya dai ita ce makomar Ukraine. Amurka ce a gaba wajen samar wa Ukraine makamai da kuma tallafi , sai Jamus da ke biye da ita. Kuma Kamala Harris ba ta taba nuna shakku ba game da ci gaba da goyon bayan Ukraine. Amurka za ta "tsaya da Ukraine da kawayenmu na NATO" kamar yadda shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz ya sha nanatawa.

A bayyane take dai Donald Trump na son kawo karshen yakin da ake yi cikin gaggawa, tare da tilastawa Ukraine ta yi watsi da manyan yankunan da Rasha ta mamaye. Bugu da kari, Harris ta bayyana matsayarta na mai goyon bayan hadin gwiwar kungiyar tsaro ta NATO tana mai cewar, a mahangar Amurka rashin hikima ne yin wani abu da zai kawo cikas ga matsayin Amurka a kawancen. A yayin da Trump ya sha yin tababa kan manufar kungiyar ta NATO. Ya kuma sha kira ga kasashen kawancen da su mayar da hankali wajen amfani da kudinsu wajen kare kansu da kansu.

Jamus | Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da Donald Trump
Shugaban gwamnatin Jamus Olaf Scholz da Donald TrumpHoto: SvenSimon/picture alliance

Bugu da kari Jamus na daya daga cikin manyan abokan kasuwancin Amurka. Don haka manufofin tattalin arzikin Washington na da babban tasiri ga Berlin. Idan Trump ya lashe zaben, ya ayyana saka harajin kaso 60 cikin 100 kan kayayyakin da Amurka ke shigowa da su daga Chaina, kana kaso 20 kan na wasu kasashen duniya. Wannan zai sa kayayyakin Jamus su yi tsada sosai a Amurka. Musamman masana'antun kera motoci da magunguna.

Sai dai a bayyana ta ke cewar, ko da wane ne ya lashe zaben a ranar 5 ga watan Nuwamba, kada Jamus ta yi tsammanin samun sassauci ga tattalin arzikinta a bangaren manufofin cinikayyarta da Amurka. Kasancewa dukkan 'yan takarar biyu suna mai da hankali ne kan karfafa masana'antu na cikin gida da yyukan yi, kamar yadda shugaban tarayyar masana'antu na Jamus, Siegfried Russwurm ya nunar a kwanan nan.