080811 London Krawalle Ermittlungen
August 9, 2011Tun bayan ɓarkewar tarzomar matasa a Tottenham a birnin London wanda ya yi sanadiyar mutuwar wani matashi mai shekaru 29 da haihuwa yayin farmakin 'yan sanda a ƙarshen mako, tarzomar ke cigaba da yaɗuwa zuwa wasu yankuna da garuruwa a wajen London inda matasan suka cinnawa gine gine da motoci wuta da kuma lalata dukiya mai tarin yawa. Ya zuwa yanzu 'yan sanda sun kama mutane fiye da 215 waɗanda ake tsare da su yayin da ake cigaba da binciken musababbin al'amarin, yadda ya faru da kuma waɗanda suka haddasa shi.
Ita dai wannan tarzoma ta faro ne sakamakon harbin da 'yan sanda suka yiwa wani matashi Mark Duggan mai shekaru 29 da haihuwa a Tottenham dake arewacin London a ranar Alhamis ɗin da ta wuce bayan da suka tsayar da Taxin da ya ke ciki yayin wani farmaki da suka ƙaddamar domin cafke mutanen dake laifuka a yankin. Wannan harbi shine ya yi sanadiyar mutuwar matashin Mark Duggan.
Mutuwar tmatashin ta haifar da ɓacin rai mai zafi a tsakanin matasa baƙaƙen fata a Tottenham wanda kuma hakan ya janyo zanga a yankin birnin da kewaye ya kuma bazu zuwa wasu sassan London da ma birane irin su Liverpool da Bristol da kuma Birmingham. A yanzu dai tuni hukumar sauraron ƙararrakin 'yan sanda ta fara gudanar da bincke akan musababbin mutuwar wannan matashi.
Mataimakin Firaministan Birtaniya Nick Clegg ya yi bayani kan wannan al'amari yana mai cewa " Abinda muka gani ya faru a ko kaɗan bai shafi mutuwar Mr Duggan ba, wanda kuma ana bincike akansa domin tabbatar da hakikanin al'amarin, amma mutane su shiga tarzoma da sata da kwasar ganima, babu hujja ko kusa ta yin wannan idan ka dubi yadda aka lalata gidajen mutane da wuraren kasuwancinsu da kuma haifar da damuwa da fannin tsaro a london baki ɗaya."
Gwamnatin Birtaniyan dai ta ce za ta yi dukkan abinda ya wajaba wajen maido da doka da oda bayan mummunan zanga zangar da aka daɗe ba'a ga irinta ba a ƙasar. Firaministan Birtaniyan David Cameron ya ce zai buƙaci majalisar dokoki ta katse hutunta na bazara a ranar Alhamis domin tattauna wannan tarzoma, ya kuma yi Allah wadai da ta'asar da ta faru.
" Yace da farko ina Allah wadai da irin abubuwan da muka gani ta akwatunan talabijin wanda mutane suka shaidar da hakan a yankunan su. Yadda aka riƙa kaiwa 'yan sanda hari da ma'aikatan kwanakwana yayin da suke ƙoƙarin kashe gobara. Wannan halayyace ta rashin ɗa'a wadda kuma wajibi ne a tunkare ta a kuma dakatar da ita."
Sai da yake tsokaci kan farmakin da 'yan sanda suka kai yankin Bakar fata a Tottenham muƙaddashin Sufeton 'yan sanda Steven Kavanagh ya yi bayani ne da cewa " Wannan ba batu ne na wata al'uma ba, amma magana ce ta wasu bata gari waɗanda ke amfani da wata dama su bata zamatakewar al'uma".
Wannan lamari dai ya haifar da muhawara a tsakanin 'yan siyasa da ma jama'ar gari. Ya zuwa yanzu 'yan sanda sun ce sun kama mutane fiye da 215 waɗanda ake tsare da su. Sai dai David Lammy wani ɗan majalisar dokoki yana mai ra'ayi da cewa
" Yawancin mutanen da aka kama ba 'yan yankin Tottenham bane mutane ne waɗanda suka zo daga wasu wurare domin haddasa fitina saboda haka ya kamata su fuskanci hukuncin shari'a."
Sima Firaministan Birtaniyan David Cameron cewa yayi wajibi ne duk wanda ya aikata ba daidai ba ya fuskanci hukunci. " Saƙo na ga waɗanda suka aikata wannan al'amari shine za ku fuskanci dukkanin hukuncin shari'a.
A yanzu dai kwamitin da aka kafa domin ya binciki musababbin mutuwar matashin da kuma dalilan da suka kai ga hakan ya ɗage zamansa zuwa ranar 12 ga watan Disamba.
Idan an duba daga ƙasa ana iya sauraron sautin wannan rahoto da kuma tsokaci akan yanayin da ake ciki a London sakamakon zanga zangar.
Mawallafa: Sebastian Hesse/Abdullahi Tanko Bala
Edita: Umaru Aliyu