Taron ƙungiyar G20 a birnin Seoul
November 11, 2010Shugabannin ƙasashen duniya suna hallara a birnin Seoul na ƙasar Koriya Ta Kudu domin taron ƙungiyar ƙasashe 20 da suka ci gaba a fannin tattalin arziƙi a duniya wato G20. A lokacin taron dai ana sa ran shugabannin ƙasashen za su tattauna batutuwan da suka haɗa da basussukan da ake bin wasu ƙasashe, da rashin daidaito wajen sha'anin cinikayya a tsakanin ƙasashen, kana da zarge zargen karya darajar kuɗin da wasu ƙasashen ke yi.
Hakanan a yayin taron ne kuma ake sa ran shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel za ta yi ƙira ga shugabannin manyan ƙasashen da ke da ƙarfin tattalin arziƙin da su tsara manufofi game da ɗaukar matakan bai ɗaya wajen kaucewa matakan da wasu ƙasashen ke ɗauka na kai ɗauki ga kamfanonin da basussuka suka kai musu iya wuya.
A halin da ake ciki kuma shugaban Amirka Barak Obama wanda ya yiwa manema labarai jawabin haɗin gwiwa tare da shugaban Koriya Ta Kudu Lee Myung-back ya bayyana fatan taron na G20 zai cimma matsaya game da hanyoyin tabbatar da ɗorewar farfaɗowar tattalin arziƙin duniya, inda kuma ya kare matakan da Amirka ke ɗauka wajen ganin ta fita daga matsalar tattalin arziƙin da take fama da ita.
Taron, wanda na yini biyu ne farawa daga yau Alhamis, zai kammala ne a gobe Jumma'a idan Allah ya kaimu.
Mawallafi : Saleh Umar Saleh
Edita : Umaru Aliyu