Taron ƙasashen G20 a Koriya ta Kudu
November 9, 2010A ranar alhamis mai zuwa ne shuagabannin ƙasashe 20 da suka fi ci gaban tattalin arziƙi a duniya zasu sake hallara a birnin Seoul, fadar mulkin Koriya ta Kudu domin gudanar da taronsu na yini biyu inda zasu yi bitar ire-iren ci gaban da aka samu dangane da matakin da suka cimma daidaituwa kansa akan sabon tsarin kuɗi na duniya. A baya ga haka zasu tsayar da wata shawara a game da tsaurara ƙai'dojin ayyukan bankuna da kuma rashin daudaituwar dangantakar cinikayya ta ƙasa da ƙasa, lamarin dake haifar da rikicin darajar takardun kuɗin ƙasashe.
Gamayyar ta ƙasashen G20, wata ƙaƙƙarfar gamayya ce da ta ƙunshi kashi biyu bisa uku na al'umar duniya da kashi casa'in cikin ɗari na tattalin arziƙin duniya da kuma kashi huɗu bisa biyar na hada-hadar ciniki ta ƙasa da ƙasa. A shekara ta 1999 ne aka ƙirƙiro gamayyar a matsayi na ministocin kuɗi na ƙasashen dake ƙarƙashin tutarta domin mayar da martani akan matsalar kuɗin da ta addabi ƙasashen Asiya da Brazil da kuma Rasha a wancan lokaci. A kuma wajejen ƙarshen shekara ta 2008 bankin nan na Lehman ya wargaje, lamarin da ya haifar da rikicin kuɗin da ya zama ruwan dare a duniyar baki ɗayanta. Nan da nan gamayyar ta G20 ta zama tamkar 'yar kwanakwana dake fafutukar kashe wannan gobara. A birnin Washington a misalin shekaru biyu da suka wuce ƙasashen suka cimma daidaituwa akan wasu jerin matakan da ya wajaba a ɗauka. An cimma daidaituwa akan cewar bai kamata a sake fuskantar irin wannan rikici ba. Domin ceto duniya daga wannan bala'in ƙasashen suka yi watsi da manufofinsu na nuna son kai. To sai dai kuma yau shekaru biyu bayan cimma wannan haɗin kai a yanzu murna tana neman komawa ciki kamar yadda Dominique Strauss-Kahn shugaban asusun ba da lamuni na duniya ya nunar:
"A ganina ɗaya daga cikin muhimman alamomin wannan rikici shi ne fahimtar da aka yi cewar wajibi ne a yi haɗin kai bisa manufa. Hakan wata sabuwar manufa ce a game da haɗin kan ma'amallar tattalin arziƙi a matsayi na ƙasa da ƙasa, wadda ba a taɓa ganin shigenta ba. An lura da wannan azamar a London da Pittsburg da Toronto. Amma kuma wajibi ne na haƙiƙance cewar wannan ci gaba ko da yake bai gushe kwatakwata ba, amma ya fara raunana. Hakan kuwa wata babbar barazana ce. Saboda wajibi ne mu ankara da cewar babu wata ƙasa ɗaya da zata iya warware wani rikicin da ya zama ruwan dare a duniya. A irin wannan hali babu wata ƙasar da zata iya yin gaban kanta."
Su kansu ƙasashen dake da hannu a gamayyar suna sane da haka. To sai dai kuma a ƙarshe ya kan zama tilas akansu su shiga gwagwarmayar shigar da shawararsu ta garambawul a majalisar dokoki ta cikin gida. A sakamakon haka shugabar gwamnatin Jamus Angela Merkel ta nuna rashin gamsuwarta da abin da aka cimma inda take cewar:
"Gwamnati ta kyautata zaton samun gudummawar cibiyoyin kuɗi wajen tinkarar rikicin da ya taso fiye da abin da ta gani."
Taron dai kamar yadda shugaban hukumar zartaswa ta Ƙungiyar Tarayyar Turai Jose Manuel Barroso ya nunar, ya zo ne daidai lokacin da ake fama da mawuyacin hali kuma zai iya zama zakaran gwajin dafi ga gamayyar ƙasashen ta G8 ko suna da ikon yin haɗin kai daidai yadda duniya ke buƙata don shawo kan matsalar dake akwai. Domin kuwa har yau dai ana fama da matsalar shingen ciniki, inda kowace ƙasa ke tunanin makomar tattalin arziƙinta kuma rashin daidatuwar da hakan kan haifar ka iya zama mafarin wani sabon rikicin nan gaba.
Mawallafi: Ahmad Tijani Lawal
Edita: Umaru Aliyu