Taron sulhunta rikicin Sudan a Saudiyya
May 7, 2023A cewar hukumomin Saudiyya wakilan bangarorin manyan hafsoshin sojan biyu da ke kokawar karbe iko wato janar Abdel Fattah al-Burhan da janar Mohamed Hamdan Daglo mai jagorantar dakarun RSF sun isa birnin na Jeddah inda ake sa ran za a cimma sabuwar yarjejeniyar tsagaita wuta don a samu damar isar da kayan agaji karkashin jagoranci Saudiyya da Amurka.
To sai dai yayin da ake laluben hanyoyin sasanta rikicin na Sudan da kawo yanzu ya yi ajalin sama da mutane 700, masu aiko da rahotanni sun ce a wannan Lahadi ma an yi ta ruwan bama-bamai a birnin Khartoum da kuma wasu sassa na kasar.
Sarki Salman ben Abdul-Aziz na Saudiyya da yarima Mohammed ben Salman sun sanar da ba da tallafi na dallar Amurka miliyan 100 domin gudanar da ayyukan jinkai a cikin kasar ta Sudan da kuma tallafa wa wadanda fadan ya sa suka yi gudun hijira.