1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron sulhu tsakanin yan adawa da gwamnatin Togo

August 8, 2006
https://p.dw.com/p/BunK

Da yammacin yau ne a birnin Ouagadougou na ƙasar Burkina Faso, a ka koma tebrin shawara tsakanin gwamnati, da yan adawar ƙasar Togo bisa jagorancin shugaba Blaise campaore.

Ɓangarorin 2, na gudanar da wannan shawarwari, da zumar samar da cimma daidaito, ta yadda ƙungiyar gamaya turai, zata maida hulɗoɗin ta, da kasar.

Ranar 26 ga watan da ya gabata, jami´yunTogo baki ɗaya su ka ɗorawa shugaban ƙasar Burkina Faso,yaunin jagorancin shiga tsakani.

Tun jiya ya fara ganawa ɗaya bayan ɗaya, da wakilan jami´yun siyasa, na adawa da masu mulki, da su ka halarci taron.

Gobe zai ci gaba da tantanawa da jama´iyar adawa UFP ta Gilchrist Olympio.

Gwamnatin ƙasar Togo, ta alkawartawa ƙungiyar EU shinfiɗa kyaukyawan tsarin demokraɗiya da kare yancin bani adama.

Tun shekara ta1993, EU ta katse hulɗoɗi da Togo, bayan ta zargi ƙasar da yin tawaye, ga tsarin mulkin demokardiya.

An fara tantanawa tsakanin jami´yun siyasar ƙasa tun ranar 21 ga watan Afrul da ya wuce, amma al´ammura su ka cije, bisa batun membobin hukumar zaɓe mai zaman kanta, da kuma ƙa´idojin zaɓen shugaban ƙasa.