1. Tsallake zuwa shafin jadawali
  2. Tsallake zuwa jadawalin abubuwan da shiri ya kunsa
  3. Tsallake zuwa karin wasu shafukan DW

Taron shugabannin CDU, CSU da kuma SPD

Mohammad Nasiru AwalOctober 7, 2005

Ba´a bayyana wani sakamako na wannan taro ba.

https://p.dw.com/p/BvZ6

Har yanzu babu tabbas game da mutumin da zai rike madafun iko a fadar shugaban gwamnatin Jamus. Ko da yake mutanen 4 sun shafe sa´o´i da dama suna tattaunawa yayin cin abincin dare a cikin ginin ´yan majalisa a birnin Berlin to amma ya zuwa yanzu batutuwan da suka yi musayar yawu akai sun kasance wani abu na sirri tsakanin yar takarar shugabar gwamnati Angela Merkel da shugaban CSU Edmund Stoiber da takwaransa na SPD Franz Müntefering da kuma shugaban gwamnati Gerhard Schröder. Domin a ranar lahadi mutane 4 zasu sake yin wata ganawa inda zasu tattauna akan batutuwa da suka hada da raba mukamai da manufofi na bai daya da mutanen da za´a ba mukaman ministoci sai kuma wanda zai dare kan kujerar shugaban gwamnati. Gabanin taron na jiya da dare shugabar CDU Angela Merkel ta yi kyakkyawan fatan cewa za´a samu masalaha game da batutuwan da suka a gaba.

“Dukkan mu mun amince cewar wannan kawance ba zai zama na jeka na yi ka ba, a´a zamu yi amfani da wannan babbar dama da ta samu don kulla wani kawance mafi a´ala ga kasarmu baki daya.”

To sai dai har yanzu ba´a kai wannan matsayi ba, domin tun jiya da rana shugaban SPD Müntefering ya ce ba za´a yi saurin bayyanawa jama´a jerin batutuwan da za´a tattauba a zauren taron ba.

“A ranar litinin da safe zamu ba da cikakken rahoto game da inda aka tsaya. Amma duk wani kokarin da za´a yi don jin wani abu daga garemu a banza ne domin mun cimma yarjejeniyar kame baki a tsakaninmu.”

Duk da haka dai yanzu a birnin na Berlin ana yada jita-jitar dangane da wadanda zasu samu mukamai a cikin gwamnati da kuma irin sassaucin da Chritian Union zata yi don shawo kan SPD ta bar ma ta kujerar shugaban gwamnati. Dole ne a samu wani daidaito wanda zai yiwa dukkan sassan biyu dadi. To sai dai samun haka zai yi wuya musamman ga Christian Union wadda sam ma ba ta son a tattauna game da mukamin shugaban gwamnati da na majalisar dokoki domin a a gareta bangaren da yafi yawan wakilai shi ke da ikon rike wadannan mukamai guda biyu.

Ko da yake a hukumance SPD ba zata so ta yi watsi da Gerhard Schröder a matsayin shugaban gwamnati ba, amma shi da kanshi ya nuna cewa ba zai zama wani karar tsaye ga wani babban kawance ba. Sannan shi kanshi shugaban SPD Müntefering ya nuna alamun sassautowa, inda ya ce zasu yi biyayya ga kowace shawarar da uwar jam´iya ta dauka.

A lokacin da yake amsa tambayoyi san da yake kan hanyar zuwa taron na jiya Schröder ya musanta jita-jitar da ake yi cewar za´a ba shi mukamin mataimakin shugaban gwamnati. Sannan a karshe yayi ba´a yana mai cewa watakila nan gaba shi za´a ba mukamin sakataren kasa a majalisar dokoki. Shi ma Edmund Stoiber da farko an ji kishin kishin cewa shi za´a ba mukamin ministan kudi daga baya aka ce a´a ministan harkokin waje amma yanzu jita-jita ake cewa shi zai zama ministan tattalin arziki.