Taron sauyin yanayi da zaben Trump a Amirka
November 9, 2016Mahalartar taron na Marrakesh sun nunar da cewa zaben da aka yi wa Donald Trump a matsayin sabon shugaban kasar Amirka, ba zai sauya komai kan yunkurin da duniya ke yi na dakile dumamar ko kuma sauyin yanayin ba. Shi dai Trump ya kasance wanda ke adawa da batun rage dumamar yanayin a duniya. Koda yake da dama daga cikin mahalarta taron sun nuna damuwarsu kan zaben da aka yi wa Trump din, saidai sun nunar da cewa zaben nasa ba zai hana aiwatar da tanade-tanaden yarjejeniyar da aka cimma a birnin Paris na kasar Faranasa ba, a watan Disambar shekarar da ta gabata ta 2015. A karkashin wannan yarjejniya dai al'ummomin kasa da kasa sun amince da rage zafin da duniya ke fama da shi da kimanin digiri biyu a ma'aunin celsius, da nufin rage barazanar da duniyar ke fuskanta.